Harin 'Yan Boko Haram Yayi Sanadiyyar Kashe Mutane 11 A Kasar Kamaru
Jami'an kasar Kamaru sun bayyana cewar wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 11 da kuma sace wasu 8 na daban a wani hari da suka kai kauyen Gakara da ke arewacin kasar a daren jiya Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wata majiyar tsaro ta kasar Kamarun tana cewa maharan dai sun iso kauyen na Gakara da ke kusa da garin Kolofata da ke arewacin kasar Kamarun da tsakar dare inda suka kona gidaje sama da 30, kana kuma suka kashe mutane akalla 11 da kuma sace wasu guda takwas, lamarin da ya tilasta wa mutanen kauyen ranta cikin na kare.
Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan Boko Haram din suke kai hari wannan kauyen da aikewa da 'yan kunar bakin wake ba, lamarin da ya sanya da dama daga cikin mutanen garin gudu da tafiya sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Kolofata wanda ke dauke da dubban 'yan gudun hijira.
Wasu rahotannin sun ce ya zuwa yanzu dai sama da mutane 20,000 ne suka mutu a kasar Kamaru kana wasu kimanin miliyan 2.7 kuma suna tarwatse sun bar gidajensu sakamakon hare-haren ta'addancin kungiyar ta Boko Haram.