Dalilin Chadi Na Katse Huldar Diflomatsiyya Da Qatar
Hukumomin Chadi sun yi bayyani kan rikicin diflomatsiyya na tsakaninsu da Qatar, wanda ya kai ga rufe ofishin jekadancin Qatar a Ndjamena.
Jagoran ýan tawayen kungiyar (UFR) Timan Erdimi wanda yanzu haka yake a zaune a kasar ta Qatar shi ne ummul aba'isin rikicin diflomatsiyya na tsakanin kasashen biyu.
Duk da cewa kungiyar ýan tawayen na Chadi ta musunta wata alaka da mahukunta Doha, amman kasar Chadi ta zargi Qatar da kokarin tada fitina a kasar tun daga Libiya.
A ranar 23 ga watan Agustan nan da muke ciki ne mahukuntan Ndjamena suka sanar da rufe ofishin jakadancin Qatar a Chadi da kuma na kasar a Doha.
Wasu majiyoyin tsaro a Ndjamna sun shaida cewan wani hari ne da aka kaiwa sojojin kasar dake sintiri a kusa da iyaka da kasar Libiya a makon jiya ne ya fusata mahukuntan Chadi har suka kai ga daukan wannan matakin.
Majiyoyi da dama sun ce tun ba yau ba ne mahukunatan Chadi ke sanya ido akan abubuwan dake faruwa da kuma halin da ake ciki a kasar Libiya da kuma Darfour, yankuna biyu da aka soma ganin ýan tawayen na Chadi.
A ýan makwanni da da suke wuce, kasar Chadi ta bukaci kasar Qatar data tuso keyar jagoran yan tawayen na Chadi mai suna Timan Erdimi, dake zaune a Doha tun cikin shekara 2009, bukatar da bata samu amsa har kawo yanzu, wanda shi ne silan rikicin diflomatsiyya na baya bayan nan na tsakanin kasashen biyu, a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Chadi, Hissein Brahim Taha.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa rikici na tsakaninsu da Qatar ba shi da wata alaka da rikicin diflomatsiya na Qatar da makoftanta Larabawa na taekun Pasha.
Ya ce Qatar da kawayenta a Libiya na kokarin tada fitina a Chadi, wanda ya ce Doha tana kare jagoran yan tawayen Erdimi wanda daga cen yake hada mutanensa, kuma daga cen din ya sha magana a kafofin yada labarai cewa yana kokarin yaki a Chadi.
A cewarsa muna ganin bai dace ba Qatar ta baiwa wani mutum irin wannan damar ba ta nuna kiyaya gare mu da kuma abubuwan dake iya tada zaune tsaye a kasarmu ba.
Saidai kungiyar ýan tawayen ta UFR ta musunta duk wani kusunci ko kuma samun taimako daga Qatar, inda wakilinta a Faransa Youssouf Hamid ya ce lalle jagoran kungiyar yana zaune a Qatar amman kungiyar ba tada hannu a harin da aka kaiwa sojojin kasar ta Chadi a makon da ya gabata.
Kuma ya ce kasancewar jagoran kungiyar a Doha, yarjejeniya ce da kasashen Chadi da Sudan suka cimma a 2009, kawai shugaba Idriss Deby da gwamnatinsa basa son fitowa karara su fadawa ýan kasar da duniya cewa suna godan bayan Saudiyya da kawayenta ne na katse hulda da Qatar, shi ne yasa su kirkiro da wannan shiri.
Kawo yanzu dai kasar Qatar bata ce uffan ba kan rikicin a hukumance, amman a ranar Alhamis da ta gabata ta sanar da rufe ofishin jekadancin Chadi a Doha tare kuma da baiwa jami''an diflomatsiyan na Chadi kwanaki uku na su fice daga kasarta, a matsayin maida martani ga kasar ta Chadi data rufe na ta offishin a Ndjamena.
Chadi dai na daga cikin kasashen Afrika da suka janye jekadunsu a Qatar a watan Yuni, kamar Senegal da Mauritaniya, biyo bayan da Saudiyya da kawayenta larabawa suka katse hulda da Qatar bisa zarginta da taimakawa ayyukan ta''andanci da kuma dasawa da Iran, batun da Qatar ke ci gaba da musuntawa.
Qatar dai ta zargi mahukuntan Riyad da kawayenta da matsin lambawa kasashen Afrika domin su ma su katse hulda diflomatsiyya da ita.