Somaliya Ta Ki Karbar Tayin Cin Hanci Domin Yanke Alaka Da Qatar
(last modified Thu, 31 Aug 2017 12:49:42 GMT )
Aug 31, 2017 12:49 UTC
  • Somaliya Ta Ki Karbar Tayin Cin Hanci Domin Yanke Alaka Da Qatar

Shugaban kasar Somalia ya ki karbar wani tayin cin hanci na dala miliyan 68 da gwamnatin Saudiyya ta gabatar masa, domin ya yanke alakar kasarsa da Qatar.

Jaridar Gulf Times ta bayar da rahoton cewa, sarkin masarautar Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya yi wa shugaban kasar Somaliya Muhamamd Abdullah Muhammad tayin cin hanci na dala miliyan 68 domin ya bi sahun kasashen da suka yanke alaka da Qatar, amma shugaban na Somalia yaki amincewa da hakan, inda ya ce a maimakonhaka da kamata ya yi Saudiyya da sauraen kawayenta su dauki matakin warware matsalarsu ta siyasa tare da Qatar ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Baya ga kin amincewa da tayin kabar cin hanci daga gwamnatin Saudiyya, shugaban na Somaliya ya sheda wa gwamnatin Qatar cewa, jiragen sama kasar za su iya yin amfani da sararin samaniya na kasar Somaliya domin yin zirga-zirga a duk lokacin da suke da bukatar hakan.