Rahotonni: Janar Khalifa Haftar Yana Shirin Kafa Gwamnati A Kasar Libiya
Rahotonni daga kasar Libiya suna bayyana cewa: Janar Khalifah Haftar babban kwamandan rundunar sojin Libiya da ke da matsuguni a garin Tobruk yana shirye-shiryen kafa wata sabuwar gwamnati a kasar Libiya.
Shafin Bauwabatu-Ifrikiyya Al-Akhabariyya ya nakalto daga ministan lafiya a gwamnatin rikon kwaryar Libiya da ke da matsuguni a garin Tobruk Ridha Al-Aukali a jiya Alhamis yana cewa: Majalisar Wakilai da kungiyoyi gami da jam'iyyun siyasa daban daban suna goyon bayan Janar Khalifa Haftar babban kwamandan rundunar sojin kasar ya kafa sabuwar gwamnati a Libiya.
Al-Aukali ya kara da cewa: Yana da imanin cewa duk wata sabuwar gwamnatin da Janar Khalifa Haftar zai kafa a Libiya zata samu karbuwa da samun goyon bayan mafi yawan al'ummar kasar saboda gagarumar nasarar da ya samu a fagen wanzar da zaman lafiya da tsaro a sassa daban daban na kasar musamman murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda.
Tun bayan da kasar Amurka da kungiyar tsaro ta NATO suka jagorancin kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi tare da kashe shi a shekara ta 2011 kasar Libiya ta fada cikin masifar tashe-tashen hankula tare da rashin samun takamammiyar gwamnatin da zata jagoranci dukkanin al'ummar kasar.