HRW Ta Zargi Sojojin Mali Da Burkina Da Cin Zarafin Bil Adama
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kada da kasa cewa da (Human Rights Watch) ta zargi sojojin Mali da Burkina faso da take hakkin bil adama a yakin da suke da mayakan dake ikirari da sunan Islama a tsakiyar kasar Mali.
A rahoton data fitar kungiyar ta ce yakin hadin gwiwar da sojojin Mali da Burkina suke yi da mayakan na Islama a tsakiyar kasar Mali a yayinsa an ci zarafin bil adama fiye da kima.
Kungiyar ta ce sojojin Mali sun aikata ba daidai ba, kana sun zartar da hukunci wanda bana shari'a ba, tare da muzgunawa da tsarewa ba bisa ka'ida ba na mutanen da ake zargi da goyan bayan mayakan masu tsatsauran ra'ayi.
Haka zalika a cewar kungiyar ta Human Right Watch sojojin Burkina Faso sun kashe wasu mutane biyu a wasni samame da suka kai a watan Yuni da ya gabata.