Aljeriya: An Kame Mutane 6 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta'addanci
Ma'aikatar tsaron kasar ta Aljeriya ce ta sanar da kame mutanen su 6 a garin Tiyaret da ke da nisan kilo mita 300 daga babban birnin kasar.
Sanarwar ma'aikatar tsaron kasar ta ce kame mutanen da aka yi ya zo ne a karkashin fada da ayyukan ta'addanci. Hudu daga cikinsu an kama su ne a jiya lahadi, yayin da aka kame biyu tun ranar juma'a.
An kuma sami abubuwa masu fashewa da kuma bama-bamai da ake jigida da su domin kai harin kunar bakin wake, a tare da mutanen. Majiyar tsaron ta ce wadanda aka kama din suna cikin 'yan ta'addar da suka koma daga Iraki da Syria.
A ranar 31 ga watan Augusta an yi taho mu gama a tsakanin 'yan sanda da wasu 'yan ta'addar da ke shirin kai harin kunar bakin wake akan ofishin 'yan sanda na garin Tiyaret. Maharin da kuma 'yan sanda biyu ne su ka mutu nan take, yayin da wani dan sanda guda ya jikkata.