Bakin Haure Sama Da Dari ne Suka Bace A Ruwan Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24239-bakin_haure_sama_da_dari_ne_suka_bace_a_ruwan_libiya
Kakakin rundunar tsaron Libiya ya sanar da bacewa bakin haure da dama bayan nutsewar kwale-kwalen da yake dauke da su a yammacin ruwan kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:43+00:00 )
Sep 21, 2017 15:29 UTC
  • Bakin Haure Sama Da Dari ne Suka Bace A Ruwan Libiya

Kakakin rundunar tsaron Libiya ya sanar da bacewa bakin haure da dama bayan nutsewar kwale-kwalen da yake dauke da su a yammacin ruwan kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ayuba Kassim mai magana da yawun dakarun tsaron ruwa Libiya a wannan alkhamis na cewa sama da bakin haure 100 ne dake kokarin zuwa kasashen Turai suka batan laya bayan nutsewar kwale-kwalen dake dauke da su a gabar ruwan garin Sabrata dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin Rundunar tsaron ruwan Libiyar ya kara da cewa a makun da ya gabata ma Dakarun tsaron ruwan kasar sun samu nasarar ceto bakin haure sama da dubu uku daga hallaka.

Duk da cewa a halin da ake ciki, an samu raguwar kwararen bakin hauren dake son zuwa kasashen Turai ba kan ka'ida ba, jami'an kasashen Libiya da Italiya sun dakile duk wasu hanyoyin da 'yan gudun hijrar ke bi domin isa zuwa kasar Italiya.

Bakin hauren dake son zuwa kasashen turai ba kan ka'ida ba na amfani da gabar ruwan garin Zawiya dake yammacin birnin Tripoli da kuma na Sabrata dake arewa maso yammacin kasar ta Libiya domin isa zuwa kasashen Turan.

Babban abin damuwa dai a nan shi ne ko wata shekara duban bakin haure ne ke rasa rayukansu cikin ruwan Mediterenia a kan hanyar su na zuwa kasashen Turai.