Rundunar Sojin Ruwan Masar Ta Karbi Wani Jirgin Ruwan Yaki Kirar Faransa
Rundunar sojojin ruwa ta kasar ta karbi wani jirgin ruwan yaki na zamani kirar kasar faransa mai suna Gowin-1
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya nakalto babban komandan sojojin ruwa na kasar Masar Ahmad Khalid yana fadar haka a jiya jumma'a a tashar jiragen ruwa ta Looyoon a kasar Faransa, sannan ya daga tutar kasar masar kan jirgin jim kadan bayan karbansa.
Kamfanin kera jiragen ruwan yaki na kasar Faransa DCNS ne ya kera jirgin yakin na Gowind-1, kuma an tsara jirgin ne don ayyukan sintiri a cikin teku. Har'ila jirgin yakin yana amfani da na'urar zamani don gani jiragen yaki na karkashin ruwa da kuma gano masu safarar mutane da kwayoyi a cikin teku. Banda haka yana daukar sojoji 80 a lokaci guda.