An Kashe Wasu Dakarun MDD Uku A Arewacin Mali
Rahotanni daga Mali na cewa a kalla sojojin Majalisar Dinkin Duniya uku ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai ma tawagar da wani abu mai fashewa a arewacin kasar.
Tawagar MDD ta Munusma a kasar ta Mali ta tabbatar da hakan inda ta sanar da mutuwar wasu sojojinta uku da kuma samun munanen raunuka ga wasu biyar a hari kwantan bauna da aka kai ma wani ayarin motoci da suke rakiya akan hanyar Anefis zuwa Gao.
Rundinar sojin kasar Bangaladash ta fitar da wata sanarwa a birnin Daka ( Dacca) cewa sojojin da suka rasa rayukansu 'yan asalin kasar ne dake cikin tawagar MDD a Mali.
Tawagar Munusma ta bakin wani kwamandanta, Koen Davids, a cikin wata sanarwa da MDD ta fitar ta yi Allah wadai da harin tare da jaddada ci gaba da aiki tare da gwamnatin Mali da bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zamen lafiyar da aka cimma a shekara 2015.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai hari kan tawagar ta MDD ba, inda ko a ranar biyar ga watan Satumban nan, wasu sojojin Munusma biyu suka gamu da ajalinsu kana wasu biyu suka ji munanan rauni a wani hari makamancin wannan a arewa maso gabashin kasar ta Mali.