Kotun Kolin Kenya Ta Bukaci A Binciki Hukumar Zabe
Kotun kolin a Kanya ta bukaci da a binciki hukumar zaben kasar akan kura kuran da aka samu a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Agustan da ya gabata.
A farkon watan Satumban nan ne dai kotun kolin kasar ta sanar da kin amuncewa da sakamakon zaben da shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyata ya lashe.
'yan adawan kasar ne dai suka shigar da kara gaban kotun wacce kuma daga bisani ta yi watsi da shi.
A zamen da ta yi yau Lahadi kotun kolin kasar ta bukaci 'yan sanda da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar ta binciki hukumar.
Nan da makwanni uku masu zuwa ne ake sa ran kammala binciken.
Wannan dai wani babban kalubale ga hukumar zaben kasar wacce tun da farko ta bayyana Uhuru Kenyata a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 54,27% a yayinda babban abokin hammayarsa Raila Odinga ya samu kashi 44,74% na yawan kuri'un da aka kada, saidai kotun ta soke zaben tare da kiran a sake shi a ranar 17 ga watan oktoba mai zuwa, kafin kuma daga bisani ta sake daga shi zuwa 26 ga watan mai shirin kamawa.