Nijar: An Kai Harin Ta'addanci A Kan Iyaka Da Kasar Aljeriya
Sep 26, 2017 19:13 UTC
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalato bayanin 'yan sandan Nijar a yau talata na cewa; Jami'an tsaro uku da farar hula guda ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harin.
An kai harin ne dai a kusa da garin Assamakka da ke arewacin kasar a kusa da iyakar kasar Aljeriya.
Bugu da kari sanarwar 'yan sandan ta ce daya daga cikinsu ya jikkata, sannan kuma maharan sun yi awon gaba da motar 'yansanda daya.
Tuni dai sojojin kasar suka fara gudanar da bincike akan abinda ya faru kamar yadda majiyar 'yansandan ta bayyana.
Kawo ya zuwa babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin.
Iyakar jamhuiryar Nijar da Aljeriya, wuri ne na zirga-zirgar masu fasa kwaurin muggan kwayoyi da kuma mutane.
Tags