HRW: Sojojin Kamaru Na Gallazawa 'Yan Gudun Hijirar Nijeriya
Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta ce sojojin kasar Kamaru sun tursasawa dubban 'yan gudun hijirar Nijeriya komawa gida bayan musgunawa da gallazawar da suka yi musu wanda hakan take dokokin kasa da kasa ne kan kare hakkokin 'yan gudun hijira.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar a yau din nan Laraba inda suka ce sojojin Kamarun su kan dauki matakan cin zarafi da suka hada da duka har ma da sauran nau'oi na keta haddi da hurumi da suka hada da fyade ga 'yan gudun hijira da suka fito daga Nijeriya kana daga baya kuma suka tilasta wa dubun dubatan 'yan gudun hijirar komawa inda suka fito.
Kungiyar ta ce ta tattauna da wasu 'yan gudun hijirar wadanda suka ce sojojin Kamaru sun gallaza musu ainun suna masu zarginsu da cewa su 'yan kungiyar Boko Haram ne ko kuma matayensu. Kungiyar dai ta ce kasar Kamaru tana daga cikin kasashen da suka kaurin suna wajen gallaza wa 'yan gudun hijira.
Sakamakon rikicin Boko Haram a Nijeriya dubun dubatan 'yan kasar ne suka gudu daga yankunan da Boko Haram din suka kama zuwa kasar Kamarun da ke makwabtaka da Nijeriya.