Uganda: Rikici A Masajisar Dokoki Dangane Da Shirin Tazarcen Shugaban Kasa.
(last modified Thu, 28 Sep 2017 06:46:10 GMT )
Sep 28, 2017 06:46 UTC
  • Uganda: Rikici A Masajisar Dokoki Dangane Da Shirin Tazarcen Shugaban Kasa.

Kwanaki biyu a jere aka dauka ana rikici a tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar ta Uganda akan kokarin da wasu ke yi na bai wa shugaba Yoweri Museveni damar yin tazarce.

Rikicin ya fara ne daga ranar talata zuwa jiya laraba akan yunkurin bai wa shugaban kasar  dama ya kara yin wani wa'adin, idan wa'adinsa na yanzu ya kare.

Shi dai Yoweri Museveni dan shekaru 72, ya dare kan karagar mulkin kasar ta Uganda ne tun 1989. Tsarin mulkin kasar ta Uganda ya tsaida shekaru 75 a matsayin shekarun karshe na shugabanci.

Za a yi zaben shugaban kasa ne a Uganda a shekara 2021, yayin da Mussevenin zai cika shekaru 76.