Gwamnatin Libya Ta Hana Amurkawa Shiga Cikin Kasarta
A jiya laraba ne gwamnatin kasar Libya ta fitar da sanarwa wacce kunshi hana Amurkawa shia cikin kasar.
Sanarwar ta yi suka ga shugaban Amurka Donald Trump bisa umarnin da ya bayar na hana 'yan kasar Libya shiga cikin kasar, tare da bayyana cewa babu abinda ya saura idan ba mayawa kura a niyarta ba.
A farkon watan Maris ne dai Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu akan umarnin hana 'yan kasashe 6 shiga cikin Amurka daga cikin hadda kasar Libya.
A ranar litinin din da ta gabata ma dai shugaban na kasar Amurka ya sake rattaba hannu akan wani sabon umarnin wanda ya sake jaddada sunayen wasu kasashe da suka hada Libya da Chadi da Korea ta Arewa, da Syria sai kuma kasashen Venezuela da Yemen.