Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Samun Hadin Kan Kasa A Kasar Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24481-majalisar_dinkin_duniya_ta_bukaci_samun_hadin_kan_kasa_a_kasar_kamaru
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci daukan matakan da suka dace domin wanzar da hadin kan kasa a kasar Kamaru.
(last modified 2018-08-22T07:00:46+00:00 )
Sep 29, 2017 15:58 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Samun Hadin Kan Kasa A Kasar Kamaru

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci daukan matakan da suka dace domin wanzar da hadin kan kasa a kasar Kamaru.

A bayanin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fitar ya bukaci mahukuntan Kamaru da su dauki matakan da suka dace da nufin warware matsalolin kasar domin ci gaba da wanzuwar hadin kan kasa a Kamaru.

Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa kan bullar zaman dardar a yankunan da suke kudu maso yamma da arewa maso yammacin kasar ta Kamaru; yana mai jaddada yin kira ga dukkanin bangarorin kasar da su nisanci duk wani abin da zai janyo bullar tashe-tashen hankula.

Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce al'ummun yankunan kudu maso yamma da arewa maso yammacin kasar Kamaru da suke magana da harshen turanci suka fara bore kan zargin gwamnatin kasar ta maida su saniyar ware, inda ake rade-raden cewa zasu shelanta ballewarsu daga kasar ta Kamaru a farkon watan Oktoba mai kamawa, sakamakon haka gwamnatin Paul Biya ta dauki matakin tura sojoji zuwa yankunan domin kalubalantar duk wani rikici.