Libiya : Rikici Ya Kashe Mutane 26 A Sabrata
A kasar Libiya mutane 26 ne suka rasa rayukansu kana wasu 170 suka raunana a mummunan fadan da aka kwashe kusan makwanni biyu ana gwabzawa tsakanin masu dauke da makamai a yankin Sabratha dake yammacin kasar.
Wadanan dai sune alkaluman farko da aka fitar a hukumance tun bayan soma rikicin a ranar 17 ga watan nan, a yankin dake nisan kilomita 70 daga yammacin birnin Tripoli.
An dai fara gwabza fadan ne bayan kisan wani mamba na mayakan dake biyaya ga Ahmad Dabbashi wani shahararen mai safara bakin haure wanda ya sauya sheka zuwa yaki da safara bakin hauren ba bisa ka'ida ba.
Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici ne tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi awan gaba da mulkin tsohin shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, wanda ya kai ga barkewar rikici tsakanin gungun dake rikice wasu iyakjokin kasar.