Sojojin Sudan Suna Ci Gaba Da Halaka A Kasar Yamen
Jaridar Akhbar ta bayyana cewa: Sojojin Sudan da suke yaki a kasar Yamen karkashin jagorancin masarautar Saudiyya suna ci gaba da shan kashi.
A rahoton da shafin Akhbar mai wallafa labarai ta hanyar Yanar gizo-gizo ya watsa a jiya Asabar ya bayyana cewa: Shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya afka cikin mummunan kangi a kasar Yamen sakamakon yadda ake kashe sojojin kasarsa.
Shafin na Akhbar ya kara da cewa: A kullum rana ana samun hasarar rayuka a tsakanin sojojin Sudan da suke yaki a kasar Yamen karkashin rundunar kawancen masarautar Saudiyya.
Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne masarautar Saudiyya ta shelanta yaki kan kasar Yamen, inda ta hada rundunar kawance daga kasashen Larabawa tare da samun cikakken goyon bayan kasar Amurka, don haka suka killace kasar ta Yamen ta sama da kasa da kuma ta ruwa lamarin da ya wurga al'ummar kasar cikin mummunan hali, inda ya zuwa yanzu aka kiyasta cewa; Al'ummar Yamen fiye da 12,000 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu dubbai suka jikkata, wasu miliyoyi kuma suka zama 'yan gudun hijira a ciki da wajen kasar.