An Gano Kaburburan Gama Gari Guda Hudu A Kasar Libya
Oct 01, 2017 19:18 UTC
Majiyar yansanda a birnin Bengazi na kasar Libya ta bayyana cewa yansandan sun gano wasu kabururruka guda hudu na gama gari wadanda suke dauke da gawawwaki kimani 80.
Kamfanin dillancin labaran Anatolio ya nakalto jami'an yansanda na Bengazi suna bada wannan sanarwan a yau Lahadi, sun kuma kara da cewa tuni an bukaci wata tawagar likitoci ta ziyarci wurin don gano masu gawawwakin.
Majiyar ta kara da cewa kungiyar yan ta'adda ta Ansarusshari'a ce ta taba iko da yankin a baya, don haka mai yuwa ita ce ta kashe wadan nan mutane ta kuma bisne su a can.
A shekarar da ta gabata ma an gano wani kabarin gama gari a wannan yankin dauke da gawawwaki kimani 72 .
Tags