Kamaru : Akalla Mutum 15 Suka Mutu A Boren Neman Ballewa
Majiyoyin asibiti a Kamaru sun ce akalla mutum 15 ne suka mutu a zanga zangar neman samun 'yanci na wasu 'yan kasar a yankunan Bamenda da Buea dake kudu maso yammacin kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan hammaya a kasar ke cewa adadin wadanda suka mutun ya kai talatin.
A halin da ake ciki dai ana ci gaba da arangama a Bamenda na yankin masu amfani da harshen Ingilishi dake arewa maso yammacin kasar inda matasa sukayi yunkurin bamkawa wani gidan sayar da man fetur mallakar gwamnati wuta, a yayin da aka jibge jami'an tsaron kai daukin gaggawa na (BIR) don murkushe masu zanga zangar.
A yankin Buea kuwa dake jiyar Kudu maso yammacin kasar jami'an tsaro na ci gaba da yi wa yankin kawanya, a yayin da mayan hanyoyin jihar ke ci gaba da kasancewa a toshe.
A jiya Lahadi ne mazauna yankin na masu amfani da harshen Ingilishi suka shelanta wani kwarya kwaryar samun 'yancin kai a daidai lokacin da kasar take bikin zagayowar ranar samun 'yanci.