Libiya : An Tsagaita Wuta A yankin Sabratha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24623-libiya_an_tsagaita_wuta_a_yankin_sabratha
Bangarorin dake rikici a yankin Sabratha na kasar Libiya sun sanar da tsagaita buda wuta, bayan shafe kwanaki na artabu tsakaninsu wanda ya janyo hasara rayukan mutane 26.
(last modified 2018-08-22T11:30:47+00:00 )
Oct 04, 2017 10:57 UTC
  • Libiya : An Tsagaita Wuta A yankin Sabratha

Bangarorin dake rikici a yankin Sabratha na kasar Libiya sun sanar da tsagaita buda wuta, bayan shafe kwanaki na artabu tsakaninsu wanda ya janyo hasara rayukan mutane 26.

galibin wadanda artabun ya rutsa da su mayakan gungun biyu ne dake dauke da makamai, saidai a acewar MDD da akwai fararen hula biyar da suka gamu da ajalisu a wannan rikici.

Yankin Sabratha dai ya shahara wanjen safara bakin haure 'yan Afrika dake kokarin tsallakawa turai.

Mutuwar wani jagoran gungun ne a wani wajen bincike da bangarorin biyu ke takkadama ya janyo rikicin.