Wani Bom Ya Fashe A Shiyar Arewa Maso Yammacin Kasar Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24641-wani_bom_ya_fashe_a_shiyar_arewa_maso_yammacin_kasar_kamaru
Mahukunta a kasar Kamaru sun sanar da fashewar wani bom a garin Bamenda da ke shiyar arewa maso yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:47+00:00 )
Oct 05, 2017 03:57 UTC
  • Wani Bom Ya Fashe A Shiyar Arewa Maso Yammacin Kasar Kamaru

Mahukunta a kasar Kamaru sun sanar da fashewar wani bom a garin Bamenda da ke shiyar arewa maso yammacin kasar.

mahukuntan kasar Kamaru a jiya Talata sun sanar da cewa: Wani bom da ake hadawa da hannu ya tarwatse a kusa da ofishin 'yan sanda da ke garin Bamenda da ke shiyar arewa maso yammacin kasar daya daga cikin yankunan da suka yi fama da tarzoma sakamakon zanga-zangar da al'ummar yankunan arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin kasar masu magana da harshen turanci suka gudanar a kokarin da suka yi na shelanta ballewa daga kasar domin kafa kasarsu mai cin gashin kai a ranar 1 ga wannan wata na Oktoba.

Majiyar tsaron kasar ta Kamaru ta bayyana cewa: Bama-bamai biyu aka ajiye a kusa da ofishin 'yan sandan da ke garin na Bamenda, daya daga cikin bom din ya fashe amma an samu nasarar lalata na biyun, ba tare da ya fashe ba, kuma babu wata kungiya ko jama'a da suka dauki alhakin dana bom din, sai dai mahukuntan kasar suna nuna yatsar zargi kan 'yan awaren kasar ta Kamaru.