Najeriya Ba Ta Goyon Bayan Takunkumin Da Saudiyya Ta Kakabawa Kasar Qatar.
Jaridar Kasar Qatar ta " al-Sharq" ta ambato ministan harkokin wajen kasar Najeriya -Geoffrey Onyeama yana kiran Saudiyya da ta kawo karshen takunkumin da ta kakabawa Qatar.
Onyeama ya ci gaba da cewa; Kakaba takunkumi ba shi ne hanyar da ta dace ba, don haka Najeriya ba ta goyon bayansa.
Kasar Saudiyya ta yi kokarin jawo hankalin kasashen Afirka da su yi wa siyasarta akan Qatar rakiya, sai dai mafi yawancinsu sun zama 'yan ba ruwanmu.
A farkon watan Yuni na wannan shekarar ta 2017 ne dai Saudiyya ta jagorancin kasashen Masar, Bahrain, da Hadaddiyar Daular larabwa, wajen yanke alakar diplomasiyya da Qatar. Bugu da kari kasashen sun kakaba mata takunkumi da hana jiragenta na sama bi ta sararin samaniyarsu.
Kasashen sun zargi Qatar da goyon bayan 'yan ta'adda, zargin da kasar ta Qatar da yi watsi da shi.