Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Dage Takunkumin Sayan Makamai Da Aka Kakaba Mata
Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ya bukaci kasashen yammacin Turai da su taimaka a dage wa kasarsa takunkumin sayan makamai da aka kakaba mata.
A zaman taron da ya gudana tsakanin fira ministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fa'iz Sarraj da jami'an rundunar sojin kungiyar tarayyar Turai a jiya Juma'a; bangarorin biyu sun tattauna kan hanyar gudanar da taimakekkeniya a tsakaninsu domin shawo kan matsalar kwararan bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku da kuma batun bada horo ga dakarun kare gabar tekun Libiya.
A yayin zaman tattaunawan a jiya Fira ministan Libiya Fa'iz Sarraj ya gabatar da bukata ga kungiyar tarayyar Turai da ta taimaka a dauki matakin dage takunkumin da aka kakaba kan kasar Libiya na hanata sayan makamai musamman ganin yadda kasar take fuskanta kalubale daga kungiyoyin 'yan ta'adda.