An Sami Raguwar Masu Son Yin Hijira Daga Nahiyar Afirka Zuwa Turai
(last modified Sat, 14 Oct 2017 11:47:42 GMT )
Oct 14, 2017 11:47 UTC
  • An Sami Raguwar Masu Son Yin Hijira Daga Nahiyar Afirka Zuwa Turai

Hukumar hijira ta kasa da kasa ta sanar da raguwar masu son zuwa ci-rani zuwa nahiyar turai.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin, ya amabato hukumar da ke kula da 'yan hijira ta duniya wacce ta fitar da bayani ta kara da cewa;  Ya zuwa ranar laraba 11 ga watan Oktoba fiye da 'yan gudun hijira dubu dari da 42 ne suka shiga kasashen Italiya, Girka, Cyprus, da Spain, ta hanyar ruwa."

A shekarar bara kuwa adadin 'yan ci-rani fiye da dubu dari uku da 18 ne suka shiga turai.

Rahoton ya kuma ci gaba da cewa; ' hanyoyi mafi aminci a wurin yan hijirar  sune gabar ruwan yammacin Afika zuwa Senigal, sai Murtaniya da Moroko sannan mashigar Jabal-Tariq

Kasashen turai suna daukar ci-ranin a matsayin kalubale mafi girma da suke fuskanta.