Gwamnatin Kamaru Ta Bada Sanarwan Fuskantar Masu Rajin Ballewa Da Karfi
Gwamnatin kasar kamaru ta ja kunnen mutanen kasar masu amfani da harshen ingilishi da su kawo karshen tashe tashen hankula da ta ce suna tayarwa a cikin yan makonnin nan, idan ba haka ba za ta yi amfani da doka wajen dawo da zaman lafiya a yankin.
Kamfanin dillancin Labaran Xinhuwa na kasar China ya bayyana cewa a cikin shekara guda da ta gabata mutanen yankin arewa da kuma kudu maso yammacin kasar Kamaru, kuma masu fafutukar samar da kasa ta masu amfani da harshen turancin ingilishi, sun yi ta gudanar da zanga-zanga don cimma manufofinsu.
Gwamnatin kasar ta Kamaru ta kara jaddada cewa ba zata yi wasa da tsaron kasar ba, don haka nauyinta ne ta kare mutuncin mutanen kasar da kuma dukkanin iyakokinta.
Tun cikin watan Nuwamban shekara ta 2016 ne mutanen kasar kamaru masu magana da harshe turacin ingilishi suke gudanar da tarurruka da kuma zanga zanga na neman ballewa daga kasar.