Lauyan Iyalan Gaddafi: Saiful Islam Gaddafi Na Cikin Koshin Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25010-lauyan_iyalan_gaddafi_saiful_islam_gaddafi_na_cikin_koshin_lafiya
Lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi, Khaled al-Zaidi ya bayyana cewar Saiful Islam Gaddafi, daya daga cikin 'ya'yan Gaddafin yana cikin koshin lafiya sannan kuma yana ci gaba da sanya ido kan lamurran siyasar kasar daga inda yake a cikin kasar Libiyan.
(last modified 2018-08-22T11:30:51+00:00 )
Oct 18, 2017 05:50 UTC
  • Lauyan Iyalan Gaddafi: Saiful Islam Gaddafi Na Cikin Koshin Lafiya

Lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi, Khaled al-Zaidi ya bayyana cewar Saiful Islam Gaddafi, daya daga cikin 'ya'yan Gaddafin yana cikin koshin lafiya sannan kuma yana ci gaba da sanya ido kan lamurran siyasar kasar daga inda yake a cikin kasar Libiyan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo lauyan Khaled al-Zaidi yana fadin cewa yana da alaka da Saiful Islam din inda ya ce yana nan yana ci gaba da ayyukansa na siyasa da kuma ganawa da kabilu da sauran masu fadi a ji, sai dai bai fadi inda yake ba, ko har yanzu yana garin na Zintan ne da ke yammacin kasar Libiyan inda aka taba tsare shi tun bayan kama shi da aka yi sakamakon kifar da gwamnatin mahaifinsa a shekara ta 2011.

A watan Yunin da ya gabata ne dai Mr. Al-Zaidin ya sanar da cewa masu rike da Saiful Islam din a garin na Zintan sun saki Saiful Islam din bayan dokar afuwa da majalisar kasar da ke gabashin kasar Libiyan ta kafa, sai dai tun lokacin ba a gan shi a bayyanar jama'a ko kuma yayi wani jawabi ba.

Wasu dai suna ganin sake Saiful Islam din yana da alaka da maganganun da ake ta yi na dawo da iyalan Gaddafin cikin harkokin siyasar kasar Libiyan a matsayin wani abin da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.