Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Jaddada Goyon Bayanta Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Kasar Iran
Shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) ya sanar da cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika tana jaddada goyon bayanta kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015.
A bayanin da shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Muhammad ya fitar ya jaddada cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika kamar sauran kungiyoyin kasa da kasa sun yi gagarumin farin ciki tare da maraba da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da manyan kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus ta ake kira da 5+1, kuma cimma yarjejeniyar tana matsayin gagarumar nasara da tattaunawa ta hanyar diflomasiyya ta yi a fagen warware sabani da takaddamar a fagen siyasar kasa da kasa.
Wannan bayanin goyon bayan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, da kungiyar tarayyar Afrika ta fitar tana matsayin maida martani kan furucin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar ne a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya bayyana yarjejeniyar da cewar ita ce yarjejeniya mafi muni da Amurka ta cimma a tsawon tarihinta, kuma yayi barazanar ficewa daga yarjejeniyar. Hakika wannan furuci na shugaban Amurka Donald Trump ya fuskanci maida martani mai gauni daga kungiyoyin kasa da kasa, gwamnatocin kasashe, masana da masharhanta daga sassa daban daban na duniya musamman kasashen yammacin Turai, inda suka jaddada wajabcin ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya da duniya ta amince da ita.
A fili yake cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika a matsayinta na wakiliyar kasashen wata nahiya durumgum a duniya, babban hakki ne da ya rataya a wuyarta ta fito fili karara ta bayyana matsayinta a harkokin da suka shafi siyasar duniya tare da jaddada wajabcin bin hanyar da ta dace da nufin wanzar da zaman lafiya da sulhu a duk fadin duniya. Kamar yadda akwai yiyuwar fassara wannan matsayi na kungiyar tarayyar Afrika da cewa: A halin yanzu ya bayyana cewa: Amurka ta zame saniyar ware a fagen siyasar duniya. Bakar siyasar Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe tare da aiwatar da bakar siyasar zalunci da babakere sun gunduri al'ummar duniya. Sannan kuma a halin yanzu duniya ta gaji da bakar siyasar yaki da zubar da jinin bil-Adama ta hanyar rungumar tafarkin warware duk wani rikici da takaddama da suka kunno kai a duniya ta hanyar diflomasiyya.
Har ila yau bayanin shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar Afrika ya jaddada wajabcin girmama wannan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya saboda yarjejeniya ce da kungiyoyin kasa da kasa, hukumomi da gwamnatocin kasashen duniya suka amince da ita, tare da daukarta a matsayin babban abin koyi a fagen warware rikici da takaddamar da ta kunno kai a fagen siyasar duniya.