'Yan Sandan Kamaru Sun Kai Hari Kan Masu Zanga-Zanga A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25093-'yan_sandan_kamaru_sun_kai_hari_kan_masu_zanga_zanga_a_kasar
Jami'an tsaron kasar Kamaru sun tarwatsa wata zanga-zanga da babbar jam'iyyar adawa ta kasar Social Democratic Front (SDF) ta shirya don nuna goyon bayanta ga al'ummomin yankunan kasar Kamarun masu magana da harshen turancin Ingilishi da suke ta neman hakkokinsu cikin watannin baya-bayan nan.
(last modified 2018-08-22T07:00:52+00:00 )
Oct 22, 2017 01:51 UTC
  • 'Yan Sandan Kamaru Sun Kai Hari Kan Masu Zanga-Zanga A Kasar

Jami'an tsaron kasar Kamaru sun tarwatsa wata zanga-zanga da babbar jam'iyyar adawa ta kasar Social Democratic Front (SDF) ta shirya don nuna goyon bayanta ga al'ummomin yankunan kasar Kamarun masu magana da harshen turancin Ingilishi da suke ta neman hakkokinsu cikin watannin baya-bayan nan.

Rahotanni daga kasar Kamarun sun bayyana cewar tun da fari dai mahukutan a kasar sun haramta zanga-zangar wadda jam'iyyar ta SDF da kuma sanannen mai fafutukan kare hakkokin bil'adama na kasar Jean-Michel Nintcheu suka kira don abin da mahukutan suka kira 'kiyaye tashin hankali da kuma lalata kayan gwamnati', sai dai kuma 'yan adawan sun yi kunnen uwar shegu da wannan haramcin.

Jami'an tsaron dai sun kama wasu daga cikin jagororin jam'iyyar ta SDF din ciki kuwa har da shi Mr. Nintcheu, bugu da kari kan wasu 'yan jarida sanannu na kasar su biyu.

Mutanen yankunan da suke magana da harshen Ingilishi din dai suna fuskantar dirar mikiya daga wajen jami'an gwamnati tun lokacin da suka fara zanga-zanga a watan Nuwamban 2016 don neman yin adalci wajen raba dukiyar kasar tsakanin yankunan kasar da kuma neman a ba su 'yancin gashin kansu, lamarin da yayi sanadiyyar kashe wasu daga cikinsu da kuma kama wasu da dama gaske.