Aljeriya : Amnesty Ta Yi Tir Da Korar Dubban 'Yan Afrika
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta yi tir da matakin hukumomin Aljeriya na korar 'yan Afrika zuwa gida.
Tun daga ranar 22 ga watan Satunban da ya gabata sama da 'yan Afrika na kudu da hamadar sahara 2,000 ne hukumomin Aljeriya suka tsare tare da tuso keyarsu zuwa kasashen Nijer da Mali.
Amnesty ta ce galibin mutanen an cafke su ne a Blida dake kusa da Aljes babban birnin kasar, inda aka kwashesu zuwa yankin Tamanrasset aka kuma yi watsi da su a kusa da iyaka da Nijer.
Kungiyar ta ce jami'an tsaron na Aljeriya basa tantance ko bakin hauren na da cikakun takardu zama ko kuma A'a, tunda dayewa daga cikinsu na da takardar bisa (Visa) da bata kare ba.
A rahoton data fitar Amensty ta bukaci hukumomin Aljeriyar dasu kawo karshen wannan kame-kame na kyammar 'yan Afrika da bai bisa ka'ida ba tare da wata wata ba.