MDD: Da Akwai Bukatar Aiki A Tsakanin Kasashe Domin Fada Da Ta'addanci
Oct 25, 2017 06:48 UTC
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Aljeriya Eric Overvest ne ya bayyana bukatar samun hadin kai a tsakanin kasashen na duniya domin kalubalantar ta'addanci.
Eric Overvest ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya wanda aka yi a birnin Alges babban birnin kasar Aljeriya, wanda ya sami halartar jakadun kasashe da dama.
Bugu da kari, wakilin Majalisar Dinkin Duniyar a kasar ta Aljeriya ya yi ishara da fadace-fadacen da suke faruwa a wasu kasashe, haka nan sauyin yanayi da suka zama gagarumin kalubale a gaban duniya.
Kasar Aljeriya tana cikin kasashen da suka fuskanci matsalar ta'addanci a shekarun baya.
Tags