MDD: Da Akwai Bukatar Aiki A Tsakanin Kasashe Domin Fada Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25158-mdd_da_akwai_bukatar_aiki_a_tsakanin_kasashe_domin_fada_da_ta'addanci
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Aljeriya Eric Overvest ne ya bayyana bukatar samun hadin kai a tsakanin kasashen na duniya domin kalubalantar ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T07:00:53+00:00 )
Oct 25, 2017 03:18 UTC
  • MDD: Da Akwai Bukatar Aiki A Tsakanin Kasashe Domin Fada Da Ta'addanci

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Aljeriya Eric Overvest ne ya bayyana bukatar samun hadin kai a tsakanin kasashen na duniya domin kalubalantar ta'addanci.

Eric Overvest ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya wanda aka yi a birnin Alges babban birnin kasar Aljeriya, wanda ya sami halartar jakadun kasashe da dama.

 Bugu da kari, wakilin Majalisar Dinkin Duniyar a kasar ta Aljeriya ya yi ishara da fadace-fadacen da suke faruwa a wasu kasashe, haka nan sauyin yanayi da suka zama gagarumin kalubale a gaban duniya.

Kasar Aljeriya tana cikin kasashen da suka fuskanci matsalar ta'addanci a shekarun baya.