Kamaru : Yaki Da Boko Haram, Ya Tsananta Talauci_ Crisis Group
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25161-kamaru_yaki_da_boko_haram_ya_tsananta_talauci_crisis_group
Kungiyar International Crisis Group, dake nazari kan rikice rikice a duniya, ta fitar da wani rahoto dake cewa yakin da ake da kungiyar Boko haram ya tsananta talauci matuka a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.
(last modified 2018-08-22T07:00:53+00:00 )
Oct 25, 2017 07:49 UTC
  • Kamaru : Yaki Da Boko Haram, Ya Tsananta Talauci_ Crisis Group

Kungiyar International Crisis Group, dake nazari kan rikice rikice a duniya, ta fitar da wani rahoto dake cewa yakin da ake da kungiyar Boko haram ya tsananta talauci matuka a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.

A rahoton data fitar kungitar ta (ICG), ta ce tun kafin zuwan Boko haram da ma yakin yana cikin tsaka mai wuya saboda talauci, aman yakin da aka shiga da kungiyar a 2014 ya kara tsananta lamarin.

Kungiyar ta bukaci da a samar da wani shiri na farfado da tattalin arzkin yankin cikin gaggawa.

Yankin arewa mai nisa na Kamaru ya kunshi yawan al'umma da ya kai miliyan hudu.