Mali: "Yan ta'adda Sun Kai Hari A Garin Soumpi
Oct 27, 2017 06:30 UTC
Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta fitar da sanarwa da ta tabbatar da kai harin a tsakiyar kasar da wata kungiya mai alaka da alka'ida ta yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; Sojoji biyu sun mutu sanadiyyar harin, sannan kuma an kone motocin soja da na fararen hula.
A ranar 23 ga watan Oktoba ma dai 'yan ta'addar sun kai hari a garin Ouan wanda ya ci rayukan sojoji biyu da jikkata guda daya.
Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro a 2012 bayan juyin mulki da kuma hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a yankunan arewacin kasar.
Faransa da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun girke sojoji a kasar ta Mali domin fada da 'yan ta'adda.
Tags