Mali: "Yan ta'adda Sun Kai Hari A Garin Soumpi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25192-mali_yan_ta'adda_sun_kai_hari_a_garin_soumpi
Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta fitar da sanarwa da ta tabbatar da kai harin a tsakiyar kasar da wata kungiya mai alaka da alka'ida ta yi.
(last modified 2018-08-22T07:00:54+00:00 )
Oct 27, 2017 03:00 UTC
  • Mali:

Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta fitar da sanarwa da ta tabbatar da kai harin a tsakiyar kasar da wata kungiya mai alaka da alka'ida ta yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; Sojoji biyu sun mutu sanadiyyar harin, sannan kuma an kone motocin soja da na fararen hula.

A ranar 23 ga watan Oktoba ma dai 'yan ta'addar sun kai hari a garin  Ouan wanda ya ci rayukan sojoji biyu da jikkata guda daya.

Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro a 2012 bayan juyin mulki da kuma hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a yankunan arewacin kasar.

Faransa da kuma  Majalisar Dinkin Duniya sun girke sojoji a kasar ta Mali domin fada da 'yan ta'adda.