Rundunar Sojin Gwamnatin Libiya Ta Gargadi 'Yan Siyasar Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25214-rundunar_sojin_gwamnatin_libiya_ta_gargadi_'yan_siyasar_kasar
Kakakin rundunar sojin Libiya ya zargi 'yan siyasar kasar da wurga kasar ta Libiya cikin matsaloli da rigingimu daban daban.
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 28, 2017 11:51 UTC
  • Rundunar Sojin Gwamnatin Libiya Ta Gargadi 'Yan Siyasar Kasar

Kakakin rundunar sojin Libiya ya zargi 'yan siyasar kasar da wurga kasar ta Libiya cikin matsaloli da rigingimu daban daban.

Ahmad al-Masmari kakakin rundunar sojin gwamnatin Libiya a jiya Juma'a ya yi gargadin cewa matukar 'yan siyasar Libiya ba su dauki matakin warware matsalolin da suke addabar al'ummar kasar ba, to fa rundunar sojin Libiya zasu dauki matakin kawo dauki birnin Tripoli fadar mulkin kasar tare da karbe iko daga hannun 'yan siyasar.

Kimanin shekaru biyu ke nan da dambaruwar siyasa ta janyo rabuwar Majalisar Dokokin Kasar Libiya zuwa biyu, daya a garin Tabruk da ke gabashin kasar, yayin da guda ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar, kuma a halin yanzu haka rundunar soji biyu ke kula da tsaron kasar.