Jama'ar Tunusiya Suna Ci Gaba Da Yin Gudun Hijira Zuwa Kasar Italiya
Ofishin kula da 'yan gudun hijira na kasa da kasa da ke kasar Tunusiya ya sanar da cewa: Daga farkon watan Satumban wannan shekara ta 2017 zuwa 18 ga wannan wata na Oktoban, 'yan kasar Tunusiya kimanin 2,900 ne suka tsallaka zuwa kasar Italiya.
Ofishin ya kara da cewa: Daga farkon watan Janairun wannan shekara ta 2017 zuwa karshen watan Ogusta bakin haure daga kasar Tunusiya kimanin 2,357 ne suka shiga cikin kasar Italiya.
Kamar yadda daga farkon wannan wata na Oktoba zuwa ranar 18 ga watan, mahukuntan Tunusiya suka hana bakin haure 1,700 kutsawa zuwa cikin kasar Italiya.
Tun bayan bullar guguwar canji da ta yi awungaba da gwamnatin Zainul-Abideen bin Ali a shekara ta 2011, ayyukan ta'addanci suka kunno kai a Tunusiya lamarin da ya janyo matsalar koma baya a harkar tattalin arzikin kasar tare da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasar kasar.