Dakarun Khalifa Haftar Sun Kai Hari Ta Sama A Gabashin Libiya
Dakarun saman kasar Libiya masu biyayya da janar khalifa haftar sun kai hari garin Derna dake gabashin kasar, lamarin da ya hallaka ko jikkata mutane sama da 30.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto majiyar asibitin kasar Libiya na cewa kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 na daban suka jikkata sanadiyar wani hari da jiragen yakin kasar suka kai garin Derna a daren jiya litinin, daga cikinsu akwai mata da kananen yara.
Garin na Derna ya kwashe tsahon lokaci karkashin killacewar dakarun tsaron kasar masu biyayya da janar khalifa haftar, tare da kai masa hare-haren ta sama, saidai akwai sabani tsakanin jami'an gwamnatin na Libiya game da irin wannan hari da sojojin kasar ke kaiwa kan al'ummar garin na Derna, inda da dama daga cikin su suka nuna adawarsu da hakan.
A karshen shekarar 2014 ne garin Derna ya fada hanun kungiyar ta'addancin IS, saidai bayan shekara guda, majalisar shawara ta masu da'awar jihadi ta samu nasarar fatattakar 'yan t'addar na IS daga cikin garin, inda yanzu garin ke karkashin ikonsu.
Sojojin kasar Libiyan na yaki ne da masu da'awar jihadin domin kwace ikon garin na Derna daga hanunsu.