Boko Haram Ta Kai Harin Ta'addancin A Arewacin Kamaru
Wata majiyar tsaron kasar kamaru ta sanar da cewa mayakan kungiyar boko haram sun kai wani harin ta'addanci a wani kauye dake arewacin kasar
Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, majiyar tsaron kasar kamaru ta ce a daren lahadin da ta gabata, mayakan kungiyar boko harm sun kai wani harin ta'addanci a kauyen Goudri na yankin Mayo-Sava dake arewacin kasar, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu da dama na daban.
Sanarwar ta ce, bayan kai harin, 'yan ta'addar ma boko haram sun gudu daga yankin.
A nasu bangare, mazauna kauyen Goudri sun bayyana cewa, wannan hari ya zo masu da bazata, saboda a ranar 28 ga wannan wata na oktoba da muke ciki, sojojin kasar sun kai wani sumame kusa da kauyen, inda suka hallaka da dama daga cikin mayakan boko haram din da suka buya a wannan yanki.