Tunisia Tana Goyon Bayan Warware Rikicin Syria Ta Hanyar Tattaunawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25263-tunisia_tana_goyon_bayan_warware_rikicin_syria_ta_hanyar_tattaunawa
Gwamnatin kasar Tunisia ta bada sanarwan cewa tana goyon bayan warware rikicin kasar syria ta hanyar tattaunawa.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Oct 31, 2017 18:48 UTC
  • Tunisia Tana Goyon Bayan Warware Rikicin Syria Ta Hanyar Tattaunawa

Gwamnatin kasar Tunisia ta bada sanarwan cewa tana goyon bayan warware rikicin kasar syria ta hanyar tattaunawa.

Kamfanin dillancin Labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Khamis Al-jahinawa ministan harkokin wajen kasar Tunisia yana fadar haka a yau Talata a birnin Tunis babban birnin kasar. Jahinawa ya kara da cewa, kasashen biyu suna da tsohuwar dangantaka a tsakaninsu, don haka yana fatan kasar syria zata sami tabbataccen zaman lafiya don su ci gaba da hulda a tsakaninsu.

A shekara ta 2012 gwamnatin kasar Tunisia ta lokacin ta katse dangantakarta da kasar Syria bisa bukatar kungiyar kasashen Larabawa, amma a cikin watan Decemban shekara ta 2014 sabuwar gwamnatin kasar ta Tunisia ta bude wani Ofishi a birnin Damascus na kasar ta Syria wanda ta kira shi ofishin kula da bukatun mutanen kasar Tunisia a Syria.

A halin yanzu dai gwamnatin kasar Syria tare da kawayenta sun sami nasara a kan yan ta'adda masu samun goyon bayan kasashen yamma da wasu kasashen yankin, wanda yasa wasu kasashen suka fara dawowa daga rikiyar yan ta'adda.