Rikici Ya Tsanata A Arewa Maso Yammacin Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25290-rikici_ya_tsanata_a_arewa_maso_yammacin_libiya
Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin khalifa haftar da sojojin gwamnatin hadin kan kasar a arewa maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:56+00:00 )
Nov 02, 2017 14:48 UTC
  • Rikici Ya Tsanata A Arewa Maso Yammacin Libiya

Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin khalifa haftar da sojojin gwamnatin hadin kan kasar a arewa maso gabashin kasar

Hakan kuwa ya biyo bayan lugudar wutar da sojojin hadin kan kasar suka yi a tungar sojojin khalifa haftar dake yankin Al-azeziya dake arewa maso gabashin kasar.

Majiyar kasar Libiyan ta bayyana cewa a ranar larabar da ta gabata Dakarun dake biyayya da gwamnatin hadin kan kasar dake birnin Tripoli sun yi lugudar wutar a yankin Al-azeziya dake arewa maso gabashin kasar.

Libiya dai ta fada cikin rikici tun bayan da kungiyar tsaron Nato ta kifar da shugaban kasar marigayyi kanar mu'amar kaddafi a shekarar 2011, a halin da ake ciki kasar Libiya nada gwamnatoci biyu da  majalisu biyu, daya a birnin Tripoli, dayar kuma birnin Trabrak dake gabashin kasar.

Gwamnatin dake gabashin kasar na samun goyon bayan sojojin dake goyon bayan khalifa haftar, yayin da gwamnatin hadin kan kasar ke gudana bisa jagorancin firaminista Fa'iz Siraj dake samun goyon bayan kasashen Duniya.