Algeria: An Kashe 'Yan Ta'adda 14 A cikin Wata Guda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25300-algeria_an_kashe_'yan_ta'adda_14_a_cikin_wata_guda
A yau juma'a me sojojin kasar ta Aljeriya suka fitar da bayani da a ciki suka bayyana kashe 'yan ta'adda 14 da kuma kame 31 a cikin wara goda.
(last modified 2018-08-22T11:30:56+00:00 )
Nov 03, 2017 11:19 UTC
  • Algeria: An Kashe 'Yan Ta'adda 14 A cikin Wata Guda

A yau juma'a me sojojin kasar ta Aljeriya suka fitar da bayani da a ciki suka bayyana kashe 'yan ta'adda 14 da kuma kame 31 a cikin wara goda.

Majiyar Sojojin kasar ta Aljeriya ta ci gaba da cewa; A cikin wata guda da ya wuce an kai hari a kan mabuyar 'yan ta'adda 30 tare da tarwatsa su, bayan gano abubuwa masu fashewa.

Bayanin ya ci gaba da cewa; wasu 'yan ta'adda sun mika kawukansu ga hukuma.

Kasar Aljeriya wacce ta ke a yankin arewacin Afrika tana zagaye da kasashen da suke fama da tabarbarewa tsaro, tana kokarin kare iyakokinta daga 'yan ta'adda.