Libya: Mafi Yawancin Mutanen Kasar Ba su Yarda Da Gwamnati Ba.
Nov 05, 2017 11:13 UTC
Sakamakon wani bincike ya tabbatar da cewa kaso 90% na al'ummar kasar ba su yarda da gwamnati ba.
Jaridar al-Qudsul-Arabi wacce ta buga sakamakon binciken ta kuma bayyana cewa kaso 79% na wadanda aka yi wa tambayoyi sun nuna bukatarsu ta ganin an kwace makaman kungiyoyin da ke kasar.
An gudanar da sakamakon ne a cikin wannan watan na Satumba a cikin garuruwa 5 na kasar a tsakanin mutane dubu daya da 211 da shekarunsu ya haura 18.
Bugu da kari, mutanen sun bayyana cewa bayan 17 ga watan Febrairu na 2011 kungiyoyin da suke dauke da makamai sun rika taka mummunan rawa a kasar.
Tags