Mataimakin Ministan Cikin Gidan Libiya Ya Tsallaka Rijiya Da Baya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25338-mataimakin_ministan_cikin_gidan_libiya_ya_tsallaka_rijiya_da_baya
Mataimakin ministan cikin gidan libiya Faraj kayyim ya tsallaka rijiya da baya, bayan da aka yi kokarin hallaka shi a birnin bangazi dake gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:57+00:00 )
Nov 06, 2017 02:23 UTC
  • Mataimakin Ministan Cikin Gidan Libiya Ya Tsallaka Rijiya Da  Baya

Mataimakin ministan cikin gidan libiya Faraj kayyim ya tsallaka rijiya da baya, bayan da aka yi kokarin hallaka shi a birnin bangazi dake gabashin kasar

Cikin wata sanarwa da firaministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fa'iz Siraj ya fitar a jiya lahadi, harin bam din da aka kaiwa tawagar mataimakin ministan cikin gidan Faraj kayyim bai yi nasara ba, domin babu mutum ko daya da ya jikkata daga cikin tawagar tasa.

Faraj kayyim mazaunin gabashin libiya ne kuma daga shekarar 2014 zuwa 2016 yayi aiki da dakarun tsaron kasar bisa jagorancin janar khalifa Haftar.

Bayan cece kucen siyasa, firaminista Fa'iz siraj ya nada Faraj kayyim a matsayin mataimakin ministan cikin gida da zai kula da al'amuran yankunan gabashin kasar dake karkashin ikon Janar Khalifa haftar.

Kasar Libiya dai ta fada cikin rikci, tun bayan kifar da gwamnatin marigayyi kanar mu'amar kaddafi a shekarar 2011,