Libya: An Kashe Sojojin Gwamnati Uku A Yankin Banighazi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25352-libya_an_kashe_sojojin_gwamnati_uku_a_yankin_banighazi
Sojojin sun mutu ne a sanadiyyar fadan da suka yi da 'yan ta'adda a ckikin birnin na Banighazi da ke gabacin kasar ta Libya.
(last modified 2018-08-22T11:30:57+00:00 )
Nov 07, 2017 06:27 UTC
  • Libya: An Kashe Sojojin Gwamnati Uku A Yankin Banighazi

Sojojin sun mutu ne a sanadiyyar fadan da suka yi da 'yan ta'adda a ckikin birnin na Banighazi da ke gabacin kasar ta Libya.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato wata sanarwa ta sojojin kasar a jiya litinin na tabbatar da mutuwar sojojin uku.

Kasar Libya ta tsunduma cikin rikici ne tun a shekarar 2011 da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato ta kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi.

Da akwai kungiyoyin masu dauke da makamai a kowace kusurwar kasar da suke fada a tsakaninsu akan madafan iko da kuma man fetur.

A gabacin kasar da akwai kungiyoyi masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda na al'ka'ida da Da'esh.