Kwamitin tsaro na MDD ya yi marhabin da tattaunawar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2536-kwamitin_tsaro_na_mdd_ya_yi_marhabin_da_tattaunawar_libiya
Kwamitin tsaro na MDD ya yi marhabin da tattaunawar bangarorin Kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 16, 2016 13:52 UTC
  • Kwamitin tsaro na MDD ya yi marhabin da tattaunawar Libiya

Kwamitin tsaro na MDD ya yi marhabin da tattaunawar bangarorin Kasar Libiya.

A wata sanarwa da ya fitar a yau, Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi marhabin da zama kan tebiri guda da bangarori daban daban na kasar Libiya suka fara da nufin magance rikicin kasar ta hanyar Siyasa, a bangare guda kuma ya bayyana damuwarsa kan yadda 'yan ta'adda suka mamaye wani bangare na kasar.

Kwamitin ya ce wannan tattaunawa da aka fara shike nuna kyakkyawar manufa da bangarorin biyu suke da ita na magance rikicin kasar.

har ila yau Manbobin kwamitin tsaro na MDD sun bukaci Gwamnatin Libiya da ta zartar da abinda ya dace domin tabbatar da tsaro a kasar

A bangare guda Babban saktaren MDD Banki Moon ya bayyana gamsuwar da yadda bangarorin kasar suka cimma matsaya na zama kan tebiri guda domin tabbatar da sulhu.