An Kashe Jami'an Jandarma A Kamaru
'Yan aware a Kamaru sun halaka jami'an jandarma biyu a bangaren kasar mai amfani da turancin Ingilishi, kwana guda bayan kisar wani jami'in tsaro.
Wasu 'yan aware a Kamaru sun halaka jami'an jandarma biyu a sashe kasar mai amfani da turancin Ingilishi, kwana guda bayan kisan wani jami'in tsaro. Kakakin gwamnatin kasar Issa Tchiroma Bakary, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP aukuwar lamarin da ya ce lamarin ya faru ne a garin Bamenda.
A cewar Tchiroma Bakary, 'yan awaren sun buda wuta kan jami'an na 'Gendarmes' ne da wasu muggan makamai lokacin da suke aikin gadin wani banki. kwana guda da aka kashe wani jami'in jandarmar a bakin makaranta Haka nan an zargin maharan da yin awon gaba da makaman jami'an.
Bamenda dai shi ne gari mafi girma a yankin arewa maso yammacin kasar ta kamaru, daya daga cikin yankunan kasar da ke fama da rikicin wariya.