MDD Ta Yi Gargadi Game Da Cin Zarafin Sojojin Faransa A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25381-mdd_ta_yi_gargadi_game_da_cin_zarafin_sojojin_faransa_a_mali
Mataimakin babban saktaren MDD a hukumar kare hakin bil-adama yayi gargadi game da cin zarafin da sojojin kasar faransa ke yi bisa da'awar yaki da ta'addancin a kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T07:00:57+00:00 )
Nov 08, 2017 14:42 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadi Game Da Cin Zarafin Sojojin Faransa A Mali

Mataimakin babban saktaren MDD a hukumar kare hakin bil-adama yayi gargadi game da cin zarafin da sojojin kasar faransa ke yi bisa da'awar yaki da ta'addancin a kasar Mali.

Yayin da yake ziyara kasar Mali a wannan laraba mataimakin babban saktaren MDD a hukumar kare hakin bil-adama Andrew Gilmour ya gargadin sojojin kasar Faransa game da cin zarafin da suke yi al'ummar kasar Mali bisa riyar yaki da ta'addanci, inda ya ce wasu ayyukan da sojojin kasar Faransar ke yi bisa da'awar yaki da ta'addanci tabbaci ne na kawar da wata al'umma da kuma take hakin bil-adama.

Mista Gilmour ya ce cin zarafin bil-adama na wakana a kasashe da dama da ake yaki da ta'addanci a cikin su.

Kafin hakan dai a jiya talata, ministan tsaron kasar mali ya bayyana da dama daga cikin sojojin kasar mali da suke hanun 'yan ta'adda sun rasa rayukansu a yayin farmakin da sojojin kasar Faransa suka kaiwa 'yan ta'addar a watan da ya gabata.

Tun bayan juyin milkin shekarar 2012 a Mali, kasar ta fada cikin matsalar rashin tsaro, inda wasu 'yan tawayen abzunawa da masu da'awar jihadi suka mamaye yankunan arewacin kasar, a tsakiyar shekarar 2013, kasar Faransa da MDD sun tura dakarunsu cikin kasar inda suka kwato yankunan da aka mamaye to saidai tun daga wancan lokaci zuwa yanzu al'ummar kasar da dama na fuskantar cin zarafi daga sojojin kasar Faransa.