Sudan : Al Bashir Zai Ziyarci Uganda
Shugaban Omar al-Bashir na Sudan, zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Uganda, wacce ita ce ta biyu tun bayan rantsar da takwaransa na Uganda Yoweri Museveni.
Ziyarar dai na da nufin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta fuskar tsaro da kasuwanci kamar yadda kafar yada labaran kasar Sudan ta rawaito.
Ziyarar shugaba al-Bashir ta kasance amsa goron gayyata ne da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya aike masa.
Rahotani sun bayyana cewa dangantaka tsakanin Sudan da Uganda ta yi matukar kyautatuwa a 'yan shekarun nan bayan da aka samu tsamin dangantakar a tsakaninsu a shekarun baya.
Kasashen Sudan da Uganda sun jima suna zargin juna da goyan bayan 'yan tawayen dake dauke da makamai.