Gobara Ta Ci Wani bangare Na Majalisar Dokokin kamaru
Nov 17, 2017 07:52 UTC
Wata gobara da aka bayyana ta faru cikin daren Jiya wayewar yau Juma'a ta ci wani bangare na ginin majalisar dokokin Jamhuriya Kamaru.
Gobara dai da ake ce ta faru ne bisa hadari ta yi mummunar barna ga ginin.
Babu dai wanda ya jikkata ko rasa ransa a gobarar.
An dai yi nasara kashe gobara bayan da 'yan kwana kwana suka shafe kusan sa'o'i shida suna kanta.
Tags