Shugaba Zuma: Kasashen Afirka Za Su Goyi Bayan Al'ummar Zimbabwe
(last modified Sat, 18 Nov 2017 16:25:20 GMT )
Nov 18, 2017 16:25 UTC
  • Shugaba Zuma: Kasashen Afirka Za Su Goyi Bayan Al'ummar Zimbabwe

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana cewar gwamnatocin kasashen Afirka za su ci gaba da goyon bayan al'ummar kasar Zimbabwe sakamakon rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar bayan da sojoji suka kwace madafun iko a kasar da kuma ci gaba da yi wa shugaban kasar Robert Mugabe daurin talala.

Shugaba Jacob Zuman ya bayyana hakan ne a yau din nan Asabar yayin da yake magana dangane da halin da kasar Zimbabwen ta shiga da kuma zanga-zangar da al'ummar suka yi don bukatar shugaba Mugaben da yayi murabus din yace yana fatan za a magance rikicin da ya kunno kai din yadda ya kamata.

Shugaban Afirka ta Kudun ya ce shugabannin kasashen Afirka za su ci gaba da goyon bayan al'ummar Zimbabwen.

A shekaran jiya ne dai shugaban kasar Afirka ta Kudun ya tura wasu ministocin gwamnatinsa zuwa kasar Zimbabwen da nufin ganawa da dukkanin bangarorin don magance rikicin da ya kunno a kasar, to sai dai kuma shugaba Mugaben ya ki amincewa da batun yayi murabus daga karagar mulkin kasar.

Tuni dai wasu shugabannin Afirkan ciki kuwa har da na kasar Botswana Ian Khama sun fara kiran shugaba Mugaben da ya sauka daga karagar mulkin kasar da yake mulkanta tun daga lokacin da ta sami 'yancin kai a shekarar 1980.